Isa ga babban shafi

Yunwa ta fara kashe mutane a zirin Gaza-MDD

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa fiye da rabin al’ummar Gaza na rayuwa ne cikin matsananciyar yunwa, kuma matsalar har ta kai yunwar ta fara daukar rayukan mutane.

Hana shigar da kayan agaji yankin ne ya haifar da yunwar
Hana shigar da kayan agaji yankin ne ya haifar da yunwar AP - Mohammed Dahman
Talla

Carl Skau, mataimakin shugaban hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya ne ya bayyana hakan, yana mai cewa a yanzu yankin Gaza baya samun kaso daya cikin uku na abincin da ya kamata ace ya shiga yankin kowacce rana.

Mr Skau ya ce yadda yakin ke kara rinchabewa kusan kowacce rana, ya haramta yanayin shigar da kayan abinci yankin.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da adadin fararen hular da Isra’ila ta kashe ya haura dubu 17, cikin watanni biyu da ta shafe tana barin wuta ta sama da kasa a zirin Gaza

Babu makawa yunwar na kara yiwa yankin kawanya ne a sakamakon hana shigar da kayan abinci da kuma kayan agaji cikin yankin da ake yiwa lakabi da budadden kurkuku, la’akari da yadda Isra’ila ta yi masa kawanya ta ko ina.

Duk da wannan matsala dai da alama babu wani mataki da duniya ke shirin dauka, don kuwa ko a taron majalisar dinkin duniya na ranar juma’a an tashi ne ba tare da samun wata matsaya ba, bayan da Amurka ta yi fatali da tayin tsagaita wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.