Isa ga babban shafi

An jinkirta musayar fursunoni tsakanin Saudiya da mayakan Houthi

A ranar Juma'a ake sa ran musayar fursunoni kusan 900 a tsakanin Saudiya da 'yan tawayen Houthi da suke gwabza yaki a kasar Yemen, jinkirin kwana guda akan sanarwar da mahukunta suka fitar tun farko. 

Wakilan kasar Saudiya, Oman da na mayakan Houthi yayin taron tattaunawar sulhu a Sanaa babban birnin kasar Yemen, ranar 9 ga Afrilun 2023.
Wakilan kasar Saudiya, Oman da na mayakan Houthi yayin taron tattaunawar sulhu a Sanaa babban birnin kasar Yemen, ranar 9 ga Afrilun 2023. via REUTERS - RYAN CARTER/UAE PRESIDENTIAL COU
Talla

Ba’a dai bayyana wani dalili na jinkirta shirin musayar fursunonin ba.

An dai tsara cewa za a shafe akalla kwanaki uku ana jigilar fursunonin a tsakanin garuruwan Yemen da makwabciyarta mai arzikin mai,wato Saudiya. 

Musayar fursunonin ita ce mafi girma da aka yi tun shekarar 2020, wadda ta zo bayan da wata tawagar Saudiya ta tattauna da 'yan tawayen Huthi na kasar Yemen da ke samun goyon bayan Iran a cikin makon nan a kokarin kawo karshen rikicin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.