Isa ga babban shafi
Yemen - Huthi

'Yan tawayen Yemen sun rufe wasu gidajen rediyon da suka ki yada farfagandar su

'Yan tawayen Huthi na kasar Yemen sun rufe gidajen rediyo shida a babban birnin kasar Sanaa, kamar yadda kungiyar 'yan jaridun kasar ta sanar, tana mai cewa matakin ya biyo bayan yadda kafafen yada labarai ke watsi da farfagandar 'yan tawayen.

'Yan tawayen houthis dake rike da arewacin Yemen da babban birnin Sanaa
'Yan tawayen houthis dake rike da arewacin Yemen da babban birnin Sanaa AP - Hani Mohammed
Talla

Mayakan Huthi masu samun goyon bayan Iran sun kwace birnin San'a daga hannun gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita a shekara ta 2014, lamarin da ya janyo yakin basasa da ya durkusar da kasar da ke fama da talauci.

Kungiyar 'yan jaridun kasar ta nakalto wata sanarwa daga gidan rediyon muryar Yeman na cewa mayakan  Huthi sun rufe gidan rediyon.

Kungiyar tace "Dakarun tsaro daga hukumomin Sana'a sun mamaye gidan rediyon a ranar Talata tare da rufe shi.

Hakazalika an rufe wasu gidajen rediyo guda biyar a birnin Sanaa, ba tare da sanar da karin bayani ba.

Sai dai 'yan jarida a birnin Sanaa sun ce 'yan Huthi sun fusata ne saboda ko dai gidajen rediyon sun ki yada farfagandar 'yan tawaye da suka hada da wake-wake na 'yan Huthi, ko kuma sun watsa kade-kade da 'yan tawayen ke ganin ya saba wa addinin Musulunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.