An kashe mutane 70 a wani hari ta sama da aka kai kan gidan Yari a Yemen
Akalla mutane 70 suka mutu a wani hari ta sama da rundunar sojojin kawancen Larabawa da Saudiya ke jagoranta ta kai kan wani gidan Yari a Yemen, yayin da kuma akalla yara uku suka mutu a wani harin bam na daban a kasar ta Yemen.
Wallafawa ranar:
'Yan tawayen Huthi sun fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna gawarwaki a cikin baraguzan ginin da farmakin jiragen yakin ya rusa, a yankin tsakiyar birnin Sa’da da ke arewacin Yemen.
Kungiyar ayyukan jin kai ta ‘Save the Children’ ta ce a wani na dabam kuma da aka kai a kudancin birnin Hodeida mai tashar jiragen ruwa, yara 3 sun mutu a lokacin da jiragen yakin kawancen sojojin Larabawa suka kai hari kan wata cibiyar sadarwa, a daidai lokacin da kananan yaran ke wasa a kusa da wurin.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rahotannin yawaitar kai hare-hare ta sama kan yankunan da ke da yawan jama'a fararen hula abu ne mai matukar tayar da hankali.
Su kuwa wasu kungiyoyin ayyukan agaji takwas da ke aiki a Yemen, sun bayyana firgita ne da labarin kashe mutane sama da 70 da suka hada da bakin haure da mata da kananan yara a gidan Yarin birnin Sa’ada, abinda suka bayyana a matsayin rashin mutunta rayukan fararen hula.
Daga bisani dai rundunar kawancen sojojin kasashen Larabawan ta musanta kai farmakin da yayi sanadin mutuwar mutane 70 a birnin Sa'da
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu