Isa ga babban shafi

Tawagar Saudiyya ta isa Yemen don tattaunawar zaman lafiya da 'yan tawaye

Tawagar Saudiyya ta isa birnin Sanaa na Yemen don tattaunawa da mahukuntan kasar game da yadda za  a cimma yarjejeniyar zaman lafiya da mayakan Huthi da ke samun goyon bayan Iran. 

Wakilan Saudiya da na 'yan tawayen Houthi a kasar Yemen, 9/04/23
Wakilan Saudiya da na 'yan tawayen Houthi a kasar Yemen, 9/04/23 AFP - -
Talla

Wannan dai na zuwa ne bayan makamanciyar ziyarar da tawagar Saudiyyan ta kai Iran ranar  Asabar da nufin tattauna yadda za a sake bude ofisohin jakadancin kasashen bayan kulle shi a shekarar 2016. 

Kafin wannan dama, sai da Ministocin Harkokin Wajen Kasashen biyu suka tattauna da juna a China, inda kuma suka sha alkawashin dai-daitawa da kuma kawo karshen yakin da ya ki ci ya ki cinyewa a Gabas ta Tsakiya. 

Wannan tattaunawar, za ta hadar da tawagar Saudiyya, Iran, Yemen da kuma Oman, wadda kuma za ta lalubo hanyoyin kawo karshen rashin jituwar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma samar da dauwamammen zaman lafiya. 

Banbancin akida na addini da kuma siyasar duniya ne dalilin da farraka tsakanin kasashen Saudiyya da Iran, abin da ake ganin yana da alaka ta kusa  da tashin hankalin da ke faruwa a kasashen Gabas ta Tsakiya, yayin da ake ganin dai-daitawar tasu za ta kawo karshen matsalar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.