Isa ga babban shafi

An gaza tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Yemen - MDD

An kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta a Yemen na tsawon watanni shida ba tare da tsawaita wa'adin ba, in ji manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bukaci a kwantar da hankula, tare da cewa ana ci gaba da tattaunawa.

Sama da mutum miliyan 23 ne suka dogara da taimakon jin kai a kasar ta Yemen.
Sama da mutum miliyan 23 ne suka dogara da taimakon jin kai a kasar ta Yemen. AFP/File
Talla

Hans Grundberg ya ce kokarin tsawaitawa da fadada yarjejeniyar tsagaita bude wuta na tsawon watanni shida bai yi nasara ba, amma dai za a ci gaba da lalubo bakin zaren.

Sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta ceba a cimma matsaya ba a yau, domin tsawaita tsagaita bude wuta zai samar da karin fa'ida mai mahimmanci ga al'ummar kasar.

"Ina kira ga bangarorin da ke rikici da juna da su cika hakkin da ya rataya a wuyan su na samar da mafita ga al'ummar Yemen wajen bin kowace hanya ta samar da zaman lafiya," in ji jami'in diflomasiyyar Sweden.

Yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka kafa na tsawon watanni biyu a watan Afrilu kuma aka sake sabunta ta har sau biyu, ta kawo koma baya a yakin da ake gwabzawa tsakanin 'yan tawayen Huthi masu samun goyon bayan Iran da kuma bangaren kawancen da Saudiyya ke jagoranta.

Yakin da ake gwabzawa tun shekara ta 2014, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da haifar da matsalar jin kai mafi muni a duniya, a cewar MDD.

Sama da mutum miliyan 23 ne suka dogara da taimakon jin kai a kasar ta Yemen.

Shawarar Grundberg ta hada da biyan albashin ma'aikatan gwamnati, bude hanyoyin shiga birnin Taez da 'yan tawaye suka yi wa katsalandan, da fadada zirga-zirgar jiragen kasuwanci daga babban birnin kasar Sana'a da kuma ba da damar karin jiragen ruwa zuwa tashar jiragen ruwa ta Hodeida dake karkashin ikon 'yan Huthi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.