Isa ga babban shafi

Harin Al-Qaeda ya hallaka 'yan tawayen Yemen 21

Akalla ‘yan tawayen Yemen 21 da wasu mambobin Al-Qaeda 6 ne suka mutu a wani harin ‘yan ta’adda irinsa na farko da kasar ta gani bayan shafe tsawon watanni karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta.

Wani mayakin 'yan tawaye a Yemen.
Wani mayakin 'yan tawaye a Yemen. AFP - NABIL HASAN
Talla

Kungiyar Al-Qaeda ta kai hari yankin Abyan da Hadaddiyar Daular Larabawa ke rike da shi a kudancin kasar ta Yemen wanda ya kai ga muayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

Harin ya zo ne kwanaki kalilan bayan ‘yan ta’addan na Al-Qaeda sun saki bidiyon da ke nuna wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya da suka yi garkuwa da shi a yankin watanni 6 da suka gabata.

Rahotanni sun ce bangarorin biyu sun gwabza fada na akalla sa’o’i 3 wanda ya kai ga mutuwar ‘yan tawayen 21 ciki har da babban jami’I yayinda a bangare ‘yan Al-Qaeda kuma mayaka 6 suka mutu, ko da ya ke wasu majiyoyi sun ce adadin wadanda suka mutun ya hauwa adadin da aka bayar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.