Isa ga babban shafi

Adadin masu fama da nakasa na yawaita a Yemen

Wata kungiyar agaji ta kasa da kasa mai suna Handicap Interational, ta ce, adadin nakasassu na karuwa a kasar Yemen bayan shafe shekaru bakwai ana yakin basasa, sakamakon hare-haren da ake kai wa a birane.

Wani yaro da ya jikkata a wani hari da jiragen yakin rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta suka kai, yana kwance a wani asibiti da ke Saada na kasar Yemen.
Wani yaro da ya jikkata a wani hari da jiragen yakin rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta suka kai, yana kwance a wani asibiti da ke Saada na kasar Yemen. AP - Hani Mohammed
Talla

Yasmine Daelman, wadda ta jagoranci wallafa rahoton na kungiyar ta Handicap International mai hedikwata a Faransa, ta ce yawan amfani da bama-bamai wajen kai hare-hare da nakiyoyi da ake binnewa, da kuma harba harsasai a wurare masu yawan jama’a, sun haifar da yawaitar yanke sassan jikin mutanen da basu ji ba, ba su gani ba da dama.

Rahotan ya kuma ce ana samun karuwar firgici da matsalar tabin kwakwalwa a tsakanin ‘yan Yemen, sakamakon yakin da ake cigaba da gwabzawa a kasar, tsakanin ‘yan tawayen Houthi da sojojin kawance da saudiya ke jagoranta.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa kimanin mutane miliyan 4.8 ne ke fama da nau’in nakasa akalla daya a Yemen daga cikin mutanen kasar miliyan 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.