Isa ga babban shafi
Yakin Yemen

Bala'in yunwa zai karu a Yemen idan aka yi watsi da ita - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya zama dole a kaucewa kuskuren mantawa da tashin hankalin da al’ummar kasar Yemen ke ciki, saboda yakin Rasha da Ukraine.

Wasu yara a sansanin 'yan gudun hijira a kasar Yemen. Ranar 12 ga Nuwamban shekarar 2018.
Wasu yara a sansanin 'yan gudun hijira a kasar Yemen. Ranar 12 ga Nuwamban shekarar 2018. REUTERS/Fawaz Salman
Talla

Majalisar ta yi gargadin ne a wannan Laraba, yayin taron da ta shirya kan cika alkawarin tallafawa gidauniyar cigaba da baiwa Yemen agaji, inda ta kara da cewar   za a fuskanci bala'i na yunwa a kasar idan ba a samu gudummawar ba.

Tun da jimawa, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana Yemen da yaki ya daidaita a matsayin kasar da aka fi fuskantar bala'in tagayyarar mutane a duniya, sai dai a yanzu karancin kudaden tallafi sun sanya munin yanayin kasar da ke ciki na kara ta'azzara.

Sansanin 'yan gudun hijirar da yakin Yemen ya tagayyara a yammacin birnin Hodeida. Ranar 6  ga watan Mayun shekarar 2020.
Sansanin 'yan gudun hijirar da yakin Yemen ya tagayyara a yammacin birnin Hodeida. Ranar 6 ga watan Mayun shekarar 2020. AFP

A wani jawabi da ya gabatar, shugaban ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths ya shaidawa manema labarai cewa, a shekarar bana kadai ana bukatar tara tallafin dala biliyan 4 da kusan rabi domin taimakawa mutane fiye da miliyan 17 a kasar Yemen.

Sai dai a yayin da kudaden tallafin ke karewa tun daga karshen shekarar da ta gabata, hakan ya tilastawa hukumomin agaji ragewa ko dakatar da ayyukan raba tallafin abinci da kiwon lafiya a kasar ta Yemen.

Wata kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewar, a cikin mutane kusan miliyan 32, miliyan 23 da kusan rabi na bukatar agajin jin kai, miliyan 12 da dubu 900 kuma na cikin tsananin bukata.

Kasar Yemen ta fada cikin kazamin yaki tun shekara ta 2014, inda ake fafatawa da 'yan tawayen Huthi masu samun goyon bayan Iran da gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita, wadanda ke samun goyon bayan kawancen sojojin kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.