Isa ga babban shafi
Yemen-Huthi

Shugaba Abedrabbo na Yemen zai mika ragamar mulki ga jagorancin hadaka

Shugaban Yemen Abedrabbo Mansour Hadi ya sanar da shirin mika ragamar mulki ga sabon shugabancin hadaka don jagorantar kasar a wani yanayi da yaki tsakanin dakarun kawancen kasashen larabawa da ‘yan tawayen Huthi ya ki ci yaki cinyewa, ko da ya ke bangarorin 2 sun aminta da tsagaita wuta saboda watan Ramadana.

Shugaba Abedrabbo Mansour Hadi, yayin wani jawabinsa a taron Majalisar dinkin duniya.
Shugaba Abedrabbo Mansour Hadi, yayin wani jawabinsa a taron Majalisar dinkin duniya. AFP/File
Talla

A wani jawabin kai tsaye da shugaba Abedrabbo Mansour Hadi ya gabatar ta gidan talabijin daga birnin Riyadh na Saudi Arabia jin kadan bayan kammala tattaunawa a zaman karshe na kokarin shawo kan rikicin na Yemen, shugaban ya ce  abun da ya zame masa wajibi a yanzu shi ne mika karfin ikonsa ga sabon jagorancin kasar.

Tuni dai Saudi Arabia ta yi maraba da matakin na Shugaba Mansour Hadi tare da sanar da shirin tallafawa kasar da agajin dala biliyan 3 ko da ya ke hadaddiyar daular larabawa ce za ta bayar da wani kaso na kudin.

Gwamnatin Hadi da ke samun goyon bayan kasashen duniya ta gamu da matsala ne sakamakon yaki da ‘yan tawayen Huthi masu samun goyon bayan Iran suka kaddamar wadanda ke rike da birnin Sanaa da kuma galibin yankunan Arewacin kasar duk da shigar Saudia wadda ta jagorancin kawancen dakarun kasashen larabawa a shekarar 2015.

Tun a 2015 ne shugaba Hadi ya bar Yemen tare da samun mafaka a Saudi Arabia lokacin da ‘yan tawayen suka kwace iko da birnin Aden mai tashar jiragen ruwa a kudancin kasar.

Karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya ne bangarorin biyu masu rikici da juna suka cimma yarjejeniyar tsagaita a asabar din da ta gabata don bayar da damar gudanar da azumin watan Ramadana, matakin da Majalisar ke cewa zai iya bude hanya ga yiyuwar sasanta rikicin baki daya duk da cewa Huthi sun kauracewa zaman tattaunawar wanda ya sanya fargabar ko za su ci gaba da kaddamar da hare-hare duk da azumin watan na Ramadana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.