Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Yemen
Ranar Asabar rundunar kawance sojin da Saudiya ke jagoranta a yakin yemen da kuma ‘yan tawayen Houthi suka ajiye makamansu, bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta gama gari, irinta ta farko tun shekarar 2016.
Wallafawa ranar:
Yarjejeniyar tsagaita wutar da bangarorin biyu suka cimma za ta shafe watanni biyu tana aiki, daga yau, ranar 1 ga watan Ramadan.
Yakin da aka shafe shekaru ana gwabzawa a Yamen ya yi sanadin mutuwar dubban mutane gami da raba wasu miliyoyi da muhallansu, lamarin da ya janyo matsalar ayyukan jin kai mafi muni a duniya, rahoton da Majalisar Dinkin Duniya.
A baya dai yarjeniyoyin tsagaita wutar da aka kulla a yakin na Yemen ba su yi wani tasiri ba.
Wata kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewar, a cikin mutane kusan miliyan 32, miliyan 23 da kusan rabi na bukatar agajin jin kai, miliyan 12 da dubu 900 kuma na cikin tsananin bukata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu