Isa ga babban shafi
Syria - ta'addanci

An tsaurara tsaro a gidan yarin da ake tsare da mayakan IS a Syria

Mayakan Kurdawa a Syria sun sake tsaurara matakan tsaro a kan gidan yarin Ghwayran  da mayakan IS suka kaiwa hari a ranakun Alhamis da Lahadin makon jiya, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane kusan 140 tare da raba wasu dubu 45 da muhallan su, saboda zargin mayakan na IS na shirin sake kaiwa gidan yarin hari.

Wani dan kungiyar ‘yan tawayen Syria na Syrian Democratic Forces yana gadi a wani gidan yari da ake tsare da wasu mutane masu alaka da kungiyar IS a arewa maso gabashin Syria a birnin Hasakeh a ranar 26 ga Oktoba, 2019.
Wani dan kungiyar ‘yan tawayen Syria na Syrian Democratic Forces yana gadi a wani gidan yari da ake tsare da wasu mutane masu alaka da kungiyar IS a arewa maso gabashin Syria a birnin Hasakeh a ranar 26 ga Oktoba, 2019. © Fadel Senna, AFP
Talla

Mayakan na kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka na sake daura damarra don tunkarar duk wani hari kan gidan yarin da mayakan na IS ka iya sake kaiwa.

Wannan dai shine hari mafi girma da muni da mayakan na IS suka kai tun shekarar 2019 da suka kai makamancin sa garin Hasakeh ranar 20 ga watan Janairun wannan shekara.

Bayanai sun ce ya zuwa yanzu an kwashe mazauna gidan yarin su dubu 3 da dari biyar tare da sauya musu matsuguni, kasancewar ‘yan ISIS din sun lalata ginin gidan yarin da kuma kwashe wasu kayayyaki masu muhimmanci.

Jagoran tawagar masu sanya Idanu kan illar da harin ya yi wato Rami Abdel Rahman ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa, kwashe mutanen daga gidan yarin ya zama wajibi, don gudun abinda ka iya faruwa idan mayakan na IS suka sake kaddamarwa gidan yarin.

A cewar Rami Rahman a yayin hare haren da Mayakan IS din suka kai, sun tafi da jami’an tsaron gidan yari da har yanzu ba’a san adadin su ba, sai dai yawan su ba zai gaza 27 ba, inda kuma wasu mutane 40 da suka hadar da ma’aikata da daurarrun gidan yarin suka bace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.