Kusan mutane 90 sun mutu yayin gumurzun mayakan IS da dakarun Kurdawa
Mutane kusan 90 sun rasa rayukansu bayan da aka kwashe akalla kwanaki uku ana gwabza fada tsakanin mayakan IS da dakarun Kurdawa a Syria, bayan da kungiyar ta IS ta kai hari kan wani gidan Yari, da aka tsare dubban mayakanta.
Wallafawa ranar:
Harin da aka kai gidan Yarin Ghwayran da ke birnin Hasakeh a arewa maso gabashin Syria, na daya daga cikin munanan hare-hare da mayakan IS suka kai a baya bayan nan, tun bayan ayyana fatattakarsu daga kasar kusan shekaru uku da suka gabata.
Shugaban kungiyar 'Syrian Observatory' da ke sa ido kan kare hakkin dan Adam a Syria, Rami Abdel Rahman, ya ce akalla jami'an tsaron Kurdawa 28, da fararen hula 5, da kuma mayakan IS 56 ne aka kashe, yayin gumurzun da aka shafe kwanaki uku ana yi.
Tun a ranar Alhamis IS ta kaddamar da farmaki kan gidan Yarin da ake tsare da wasu mayakanta da adadinsu ya kai akalla dubu 3 da 500, ciki har da wasu shugabanninta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu