Isa ga babban shafi
Syria

Mayakan IS sun kashe jami'an tsaron Kurdawa 18 a gidan Yarin Syria

Jami’an tsaron Kurdawa akalla 18, ciki harda masu gadi, aka kashe a wani harin da kungiyar IS ta kai kan gidan yarin Syria da ke dauke da dubban mutanen da ake tuhumarsu da zama mayaka masu ikirarin jihadi.

Wani dan kungiyar ‘yan tawayen Syria na Syrian Democratic Forces yana gadi a wani gidan yari da ake tsare da wasu mutane masu alaka da kungiyar IS a arewa maso gabashin Syria a birnin Hasakeh a ranar 26 ga Oktoba, 2019.
Wani dan kungiyar ‘yan tawayen Syria na Syrian Democratic Forces yana gadi a wani gidan yari da ake tsare da wasu mutane masu alaka da kungiyar IS a arewa maso gabashin Syria a birnin Hasakeh a ranar 26 ga Oktoba, 2019. © Fadel Senna, AFP
Talla

Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria, ta ce jami’an tsaron Kurdawa sun samu nasarar kashe mayakan na IS akalla 16 a fadan da aka gwabza a daren ranar Alhamis a gidan yarin Ghwayran.

‘Syrian Observatory’ da ke sa ido kan yakin kasar Syria ta bayyana farmakin da IS ta kai gidan Yarin, a matsayin hari mafi muni tun bayan da aka shelar fatattakar 'yan ta'addan na IS cikin shekarar 2019 a kasar ta Syria.

Gidan Yarin Ghwayran da ke birnin Hassakeh a arewa maso gabashin Syria yana dauke da mutane kusan dubu 3,500 da ake zargin 'yan kungiyar IS ne da suka hada da wasu manyan shugabannin kungiyar, kuma fadan na ranar Juma'a ya zo ne a daidai lokacin da fursunonin na IS ke kokarin tserewa daga sansanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.