Isa ga babban shafi
Jamus-Syria

Kotun Jamus ta yi wa wani Kanar din Sojan Syria daurin rai da rai

Wata kotu a Jamus ta yanke wa tsohon Sojan kasar Syria hukuncin daurin rai da rai, sakamakon kama shi da laifin azabtar da bila’adama da kisan kai, a wata shari’a mai tarihi a kasar.

Kanar Anwar Raslan, yayin gurfanarsa gaban Kotun Jamus.
Kanar Anwar Raslan, yayin gurfanarsa gaban Kotun Jamus. AFP - THOMAS LOHNES
Talla

Kotun dai ta yankewa Kanar Anwar Raslan mai shekaru 58 hukuncin daurin rai da rai ne bisa kama shi da laifin azabtarwa da kuma hallaka mutane 27 ba bisa ka’ida ba a gidan yarin Al-Khatib dake birnin Damascus a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2012.

Anwar Raslan ya kuma nemi mafakar siyasa a Jamus a shekarar 2012 lokacin da aka fara zargin sa da yunkurin cin amanar kasar.

Masu shigar da kara dai, sun kuma tuhumi Anwar da kin tsawatar wa yayin da aka hallaka mutane 58 tare da azabtar da sama da dubu 4 duk a gidan yarin na Al-Khatib.

An dai gabatar da shaidu sama da 80 cikin su har da guda 12 da aka fara zargin su tare da cin amanar kasar, da kuma ‘yan kasar ta Syria da ke zama a kasashen turai da dama don bada shaida akan sa.

Tuni dai shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch Kenneth Roth ya yi maraba da hukuncin, yana mai cewa a yau wadanda suka rasa rayukan su a karkashin sanya idanun sa, ba tare da hakkin su ba sun sami adalci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.