Isa ga babban shafi
Spain

Puidgemont zai gurfana gaban kotun Jamus

Tubabben shugaban yankin Catalonia Carles Puidgemont zai gurfana gaban kotun Jamus a gobe Litinin don amsa tuhume-tuhume da ake masa kan rawar da ya taka a kada kuri'ar ballewar yankinsa daga Spain da nufin kafa kasa mai cin gashin kai.

Matukar dai Carles Puidgemont ya amsa dukkanin zarge-zargen da Spain ke masa babu shakka zai iya fuskantar daurin shekaru a gidan kaso.
Matukar dai Carles Puidgemont ya amsa dukkanin zarge-zargen da Spain ke masa babu shakka zai iya fuskantar daurin shekaru a gidan kaso. REUTERS/Scanpix Denmark/Tariq Mikkel Khan
Talla

A yau Lahadi ne dai Carles Puigdemont, ya shiga hannun 'yan sandan kasar Jamus  bayan da ya ratsa kasar daga Danemark a ziyarar da ya kai kasar Finland da nufin ganawa da wasu 'yan majalisun kasar.

Jamus dai ta kame tubabben shugaban ne karkashin sammacin kamashi da Spain ta gabatarwa hukumar yan sanda kasa da kasa tun bayan da ya fara gudun hijira a Belgium lokacin da gwamnatin Spain da hambarar da shugabancinsa tare da nadin sabbin shugabanni baya ga kame wasu manyan mukarrabansa.

Tuni dai dubban al'ummar Catalonia suka fara zanga-zanga kan matakin a kasar ta Spain, ko da ya ke dai kakakin jam'iyar 'yan awaren na Catalonia ne Anna Grabalosa ta sanar da cewa tubabben shugaban na cikin koshin lafiya.

Matukar dai Puidgemont ya amsa dukkanin tuhume-tuhumen da Spain ke yi kansa babu shakka zai iya fuskantar daurin shekaru a gidan yari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.