Isa ga babban shafi
Syria

Amurka ta sake kashe wani babban kwamandan al-Qaeda a Syria

Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon, ta sanar da kashe wani babban jagoran kungiyar Al-Qaeda yayin wani hari da jiragen yakin kasar marasa matuka suka kai a Syria.

Wani jirgin sama mara matuki mallakin Amurka.
Wani jirgin sama mara matuki mallakin Amurka. AFP - HANDOUT
Talla

Harin ya zo ne kwanaki biyu bayan farmakin da aka kai kan wani sansanin dake kudancin Syria, wanda kawancen da Amurka ke jagoranta ke amfani da shi wajen yakar kungiyar IS.

Kakakin rundunar kawancen da Amurka ke jagoranta a Syria Manjo John Rigsbee ya tabbatar da nasarar da suka samu wajen kashe Abdul Hamid al-Matar babban shugaban kungiyar ta al-Qaeda.

A karshen watan Satumba Pentagon ta kashe Salim Abu-Ahmad, wani babban kwamandan na Al-Qaeda a Syria, a wani hari ta sama da dakarunta suka kai kusa da Idlib a arewa maso yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.