Amurka ta dauki alhakin harin da ya kashe mutane a Syria
Kasar Amurka ta ce ita ta kai wani kazamin harin da ya kashe fararen hula sama da 40 a wani Masallaci da ke Idlib a yankin arewacin Syria.
Wallafawa ranar:
Kakakin rundunar sojin kasar, Kanar John J Thomas ya tabbatar da kai harin, amma ya ce ba wai Masallaci suka shirya kai shi ba, sai dai wani ginin sansanin mayakan Al Qaeda.
Jami’in ya ce za su gudanar da bincike kan zargin mutuwar fararen hula.
Shugaban kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam a Syria, Rami Abdel Rahman ya ce, wasu jiragen yaki ne da a fayyace su ba suka kaddamar da farmakin kan masallacin a dai dai lokacin da ake gudanar da sallar magariba.
Rahman ya ce, harin ya fi ritsa wa da fararen hula kuma akwai wadanda baraguzan ginin masallacin suka binne, baya ga sama da 100 da suka jikkata.
Rundunar hadaka da Amurka ke jagoranta wajen yaki da mayakan jihadi ta kai hare-haren da suka ritsa da fararen hula a Syria da Iraqi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu