Isa ga babban shafi
Syria

Kasashen Yamma sun bukaci zaman sasanta rikicin Syria

Manyan kasashen Yammacin duniya sun bukaci maido da zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin Syria da ‘yan tawaye don kawo karshen rikicin da ya lakume rayukan jama’a fiye da dubu 300. 

Manyan kasashen Yammacin duniya na tattaunawa kan yadda za a magance rikicin Syria da ya lakume rayuka fiye da dubu 300
Manyan kasashen Yammacin duniya na tattaunawa kan yadda za a magance rikicin Syria da ya lakume rayuka fiye da dubu 300
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka da ya gana da ‘yan tawayen a birnin Paris na Faransa John Kerry, ya bayyana hare-haren da dakarun gwamnatin Syria ke kai wa birnin Aleppo a matsayin laifukan yaki da kuma cin zarafin bil’adama.

Mr. Kerry ya kuma bukaci Rasha da sauran magoya bayan shugaba Bashar al Assad da su taimaka wajen kawo karhen rikicin.

Ministan harkoin wajen Faransa, Jean Marc Ayrault ya bayyana cewa, ‘yan tawayen sun sanar da shirinsu na komawa kan teburin tattaunawa ba tare gindaya wasu ka’idoji ba.

Ita ma kasar Jamus ta bukaci dakarun Syria da su bude wa faraen hula hanyar ficewa daga birnin Aleppo mai fama da hare-hare.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.