Isa ga babban shafi
Syria

Rasha da China sun yi watsi da matakin kuntata wa Syria

Kasashen Rasha da China sun yi watsi da kudirin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya samu goyon bayan kasashen Yamma don ganin an sanya wa Syria takunkumi sakamakon amfani da makamai masu guba.

Kwararrun Jami'an tsaro da ke bincike game da makami mai guba da aka yi amfani da shi a yakin Syria
Kwararrun Jami'an tsaro da ke bincike game da makami mai guba da aka yi amfani da shi a yakin Syria REUTERS/Mohamed Abdullah/Files
Talla

Kudirin wanda kasashen Birtaniya da Faransa da Amurka suka gabatar da shi ya samu kuri’un kasaashe 9 da suka amince da shi a zauren kwamitin sulhun, yayin da China da Rasha da Bolivia suka ki amince wa da kudirin.

Su kuwa kasashen Kazakhstan da Habasha da Masar sun kaurace wa kada kuri’ar, yayin da kudirin ke bukatar kuri’u 9 ba tare da kuma samun koda kasa guda da za ta nuna adawa ba kafin aiwatar da shi.

A karo na bakwai kenan da Rasha wadda ta kasance kawa ga Syria ta fannin soji ke amfani da karfin kujerarta don kare gwamnatin shugaba Bashar al Assad.

Ita ma dai China mai kujerar din-din-din a kwamitin ta bi sahun Rasha wajen kin amince wa da kudirorin guda 6 kan kasar ta Syria.
 

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya gargadi cewa, sanya takunkumai kan Syria a dai dai wannan lokaci na zaman tattaunawar sulhu a birnin Geneva bai dace ba, kuma hakan zai iya haifar da cikas a kokarin da ake yi na kawo karshen rikicin kusan shekaru shida a kasar.

Sai dai jakadiyar Amurka a Majalisar, Nikki Haley ta ce, wannan matakin ya yi dai dai duk da dai bai samu karbuwar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.