Isa ga babban shafi
Syria

Amurka ta kashe wani kwamandan Al Qaeda a Syria

Ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta sanar da kashe wani babban Kwamandan kungiyar Al Qaeda mai suna Muhsin Alfadli lokacin wani harin sama da jiragen Amruka suka kai a yankin Sarmada da ke cikin Syria.

An kashe Muhsin Al Fadhli ne tun a ranar 8 ga watan Yuli a Syria
An kashe Muhsin Al Fadhli ne tun a ranar 8 ga watan Yuli a Syria REUTERS
Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka Kaftin Jeff Davis ya ce a ranar 8 ga wannan wata na Yuli ne suka kai harin, kuma daga bisani sun tabbatar da mutuwar Kwamandan da ke jagorantar kungiyar Khorasan, reshn kungiyar Al Qaeda.

Fadhli wanda aka ce dan asalin kasar Kuwait ne, yana cikin manyan kwamandojin shugaban Al Qaeda marigayi Osama bin laden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.