Isa ga babban shafi
SYRIA

An kashe magoya bayan Al-Nosra 25 a yankin Idlib na Syria

Rahotanni daga Syria, na cewa magoya bayan kungiyar Al Nusra, reshen Alqa’ida da ke kasar su akalla 25 ne suka rasa rayukansu sakamokon fashewar bam a wani masallaci da ke birnin Ariha na lardin Idlib.

Marat al-Numan, arewacin yankin Idlib cikin watan oktoban 2012
Marat al-Numan, arewacin yankin Idlib cikin watan oktoban 2012 REUTERS
Talla

Rami Abdel Rahman shugaban Kungiyar da ke sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Syria, ya ce mai yiyuwa ne adadin wadanda suka rasa rayukansu ya zarta hakan, domin kuwa akwai wasu da dama da suka sami munanan raunuka sakamakon wannan fashewa.

Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da daruruwan mutane suka taru a masallaci domin buda bakin azumin ranar jiya juma’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.