ISIL ta kashe sama da mutane dubu 3 cikin shekara 1 a Syria
Kungiyar IS a kasar Syria ta kashe mutane sama da dubu 3 a kasar cikin shekara 1, kuma mafi yawansu fararen hula ne da kanana yara, tun daga lokacin da ta kaddamar da hare-haren ta a kasar, kamar yadda kungiyar nan dake sa’ido a harkokin kasar ta sanar.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta ce tun ranar 29 ga watan yunin bara kawo yanzu , mayakan jihadin da ke ikrarin kafa daular Islama a yankin gabas ta tsakkiya sun kashe kimanin mutane 3,027 a Syria.
Daga cikin mutanen da kungiyar ta kashe sun hada da fararen hula 1718 kuma 74 daga cikinsu kananan yara ne
Mutanen da ISIL ta fi kashewa dai sune 'yan kabilar Shaitat 'yan sunni, da suka kasance rabin adadin mutanen da Mayakan suka hallaka, sai wasu mutanen 930 'yan kabilar Deir Ezzor, a gabashin kasar wadanda suka nuna wa Mayakan turjiya..
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu