'Yan Syria sun kona litattafan Turkiyya saboda batanci ga Annabi
Wasu litattafai da Ma’aikatar Ilimi ta Turkiya ta samar tare da rarraba su a arewacin Syria, sun janyo fushin al’umma saboda yadda suke dauke da zanen kwatancen Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi Wasallam, yayin da jama’a suka kona litattafan.
Wallafawa ranar:
Al’ummar Musulmin duniya na girmama Annabi Muhammad, kuma suna daukar duk wani wargi da aka yi masa a matsayin gingimemen laifi ko kuma sabo.
Littafan na addini da Ma’aikatar Ilimin Turkiya ta wallafa domin ilmantar da yara a wasu yankuna na Syria dake karkashin ikon gwamnatin Ankara, na dauke da zane-zanen da jama’ar yankin suka bayyana a matsayin cin mutuncin addini.
A can birnin Jarablus, kusa da kan iyakar Turkiya, jama’a sun kona daukacin littafan da suka zo hannunsu kurmus kamar yadda wasu fayafayen da aka watsa a shafukan sada zumunta suna nuna.
Daya daga cikin mazauna yankin na Jarablus, Mustafa Abdulhaq ya ce, lallai sun kadu matuka da ganin wadannan littafai masu munin gaske, dalilin ya sa suka kona su a cewarsa.
Kazalika al’ummar birnin Al-Bab sun lashi takobin gudanar da zanga-zanga a yau Juma’a mudin ba a shafe wadannan kazaman littafai baki daya ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu