Isa ga babban shafi
Syria-Kurdawa

Mayakan Kurdawa sun kashe mutane 136 a hari kan gidan yarin Syria

Yawan mutanen da suka hallaka sakamakon harin da mayakan kurdawa suka kai kan wani gidan yari da ke kasar  Syria ya kai 136, cikin su har da farafen hula.

Wasu mayakan Kurdawa a Syria.
Wasu mayakan Kurdawa a Syria. AFP
Talla

Fiye da mayakan kurdawa 100 ne suka kai hari kan gidan yarin ranar Alhamis, da nufin kubutar da mambobin kungiyar su da ake tsare da su a gidan yarin, a wani hari mafi muni da mayakan suka kai tun shekaru 3 da suka gabata.

Bayan kubutar da daurarrun gidan yarin sun kuma afkawa ma’aikatan gidan yarin, tare da kwatar makamai da sauran kayayyakin aiki masu muhimmanci, kamar yadda wata kungiyar kare hakkin dan Adam a kasar ta tabbatar.

Bayanai sun ce cikin mutanen da aka tabbatar da mutuwar su zuwa yanzu akwai mambobin kungiyar IS guda 84 sai na mayakan kurdawa guda 45 a ciki da wajen gidan yarin, a yayin da farafen hula 7 suma suka kwanta dama.

Ya zuwa yanzu dai dakarun kasar ta Syria sun kulle duk wasu mashigun gidan yarin sakamakon yadda mayakan suka sake komawa a ranar lahadi tare da luguden wuta ta sama, wanda hakan ya kara yawan adadin wadanda suka halakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.