Isa ga babban shafi
Syria

IS ta kashe jami'an tsaron gidan yarin Syria

Jami’an tsaron Kurdawa akalla 18, ciki har da masu gadi aka kashe a wani hari da kungiyar IS ta kai kan gidan yarin Syria da ke dauke da dubban mutanen da ake tuhumar su da zama mayaka masu ikirarin jihadi.

Wasu daga cikin wadanda suka jikkata a harin da IS ta kai Syria
Wasu daga cikin wadanda suka jikkata a harin da IS ta kai Syria © APAnsar Allah Media Office via AP
Talla

Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria, ta ce jami’an tsaron Kurdawa sun samu nasarar kashe mayakan na IS akalla 16 a fadan da aka gwabza a daren ranar Alhamis a gidan yarin Ghwayran.

‘Syrian Observatory’ da ke sa ido kan yakin kasar Syria ta bayyana farmakin da IS ta kai gidan yarin a matsayin hari mafi muni tun bayan da aka yi shelar fatattakar 'yan ta'addan na IS cikin shekarar 2019 a kasar ta Syria.

Gidan yarin da ke birnin Hasakeh a arewa maso gabashin Syria yana dauke da mutane kusan dubu 3,500 da ake zargin 'yan kungiyar IS ne da suka hada da wasu manyan shugabannin kungiyar, kuma fadan na ranar Juma'a ya zo ne a daidai lokacin da fursunonin na IS ke kokarin tserewa daga sansanin.

Kungiyar IS dai ta sha kai hare-hare kan Kurdawa da kuma cibiyoyin gwamnatin Syria, tun bayan fatattakar 'yan ta'addan da aka yi a watan Maris na shekarar 2019 a kasar ta Syria, kuma a akasarin lokuta mayakan suna kai farmaki ne kan sojoji da kuma cibiyoyin man fetur, abinda ya sanya fasa gidan Yarin Hasakeh ya zama wani sabon salon da mayakan na IS suka fito da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.