Isa ga babban shafi
Syria - IS

Harin IS kan gidan yarin Syria ya tagayyara mutane dubu 45

Akalla mutane dubu 45 suka rasa muhallansu a kasar Syria bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin mayakan IS da dakarun Kurdawa tsawon kwanaki 3, a lokacin da kungiyar ta IS ta kaddamar da farmaki kan gidan Yarin Ghwayran a ranakun Alhamis zuwa Lahadin makon jiya.

Wasu daga cikin dubban fararen hular da suka tsere daga muhallansu sakamakon kazamin fadan da aka gwabza tsakanin mayakan IS da dakarun Kurdawa.
Wasu daga cikin dubban fararen hular da suka tsere daga muhallansu sakamakon kazamin fadan da aka gwabza tsakanin mayakan IS da dakarun Kurdawa. © AFP - -
Talla

Kazamin fadan da aka fafata tsakanin bangarorin biyu dai yayi sanadin halaka mutane fiye da 140, ciki har da fararen hula.

Tun da fari mayakan na IS sun kai harin ne da nufin kubutar da mambobinsu da ke tsare a gidan Yarin mai matukar tsaro, lamarin da ya juye zuwa kazamin gumurzu da ya lakume rayukan mutane da dama.

Bayan barnar kisan kai mayakan sun yi awon gaba da kayayyakin aikin jami’an tsaron gidan Yarin da kuma wasu muhimman takardu da ke kunshe da wasu bayanai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.