Isa ga babban shafi
Iraqi

Harin bam ya kashe mutane 4 a Iraqi

Akalla fararen hula hudu ne suka mutu yayin da wasu hudu suka jikkata a ranar Talata, sakamakon wani harin bam da aka kai da babur a kusa da wani asibiti da ke tsakiyar birnin Basra a kudancin kasar Iraqi.

Jami'an tsaron Iraqi yayin duba wurin da bam ya fashe a Basra, a ranar 7 ga Disamba, 2021.
Jami'an tsaron Iraqi yayin duba wurin da bam ya fashe a Basra, a ranar 7 ga Disamba, 2021. © REUTERS/Mohammed Aty
Talla

Kawo yanzu dai babu wanda ya yi ikirarin kai harin a birnin na na Basra, wanda a shekarun baya-bayan ya sha fama da hare-hare.

Sai dai a makwannin da suka gabata an kai munanan hare-hare kan mayakan Kurdawa a arewacin Iraqi, wadanda IS ke ikirarin kaiwa.

Hare-haren ta’addanci da kuma tsananin yaki sun tagayyara kasar Iraqi tsawon shekaru tun bayan da Amurka ta mamaye kasar tare da kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Saddam Hussein a shekara ta 2003.

Mayakan IS a yayin da suke gudanar da faretin soji a kan titunan lardin Raqqa da ke arewacin kasar Iraqi a hoton ranar 30 ga watan Yunin 2014.
Mayakan IS a yayin da suke gudanar da faretin soji a kan titunan lardin Raqqa da ke arewacin kasar Iraqi a hoton ranar 30 ga watan Yunin 2014. REUTERS/Stringer

Idan za a iya tunawa dai, IS ta taba kafa shugabancinta a yankuna masu fadi da ke Syria da Iraki daga shekara ta 2014, amma daga bisani yankunan suka kubuce mata, sakamakon murkushe kungiyar da dakarun sojin Iraqi suka yi tare da taimakon Amurka da kungiyar tsaro ta NATO.

A 9 ga watan Disamba ba shekarar. 2017, rundunar sojojin Iraqi ta sanar da samun nasarar mayakan kungiyar IS da ke ikirarin Jihadi.

Sai dai har yanzu mayakan na IS na ci gaba da zama a asirce a kasashen na Iraqi da Syria, inda suke kai hare-hare kunar bakin wake cikin salon yakin ‘sari ka noke’

Hari mai muni na baya bayan nan da IS ta dauki alhakin kaiwa a Iraqi shi ne wanda aka kai kan wata kasuwa da ke unguwar ‘yan Shi’a a unguwar Sadr da ke Bagadaza a watan Yuli, inda aka kashe mutane kusan 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.