Isa ga babban shafi
Iraqi - Ta'addanci

Iraqi: An sake kai harin bam kan kasuwa a birnin Bagadaza

Hukumomin tsaro da na lafiya a Iraqi, sun ce akalla mutane 4 sun mutu, yayin da wasu 17 suka jikkata a yankin Sadr dake birnin Bagadaza, bayan tarwatsewar bam din da aka nada a wata mota a ranar Alhamis.

Jami'an tsaron Amurka yayin sintiri a daya daga cikin titunan birnin Bagadaza.
Jami'an tsaron Amurka yayin sintiri a daya daga cikin titunan birnin Bagadaza. ASSOCIATED PRESS - Hadi Mizban
Talla

Yayin karin bayani kan harin, ‘yan sanda sun ce an ajiye motar da ta tarwatse ne a wata kasuwar saida kayayyakin da aka taba amfani da su dake yankin da mabiya mazhabar shi’a suka fi yawa.

Harin na yau Alhamis na zuwa ne a yayin da ake hamayya ta zafafa tsakanin jam’iyyun siyasar Iraqi, sakamakon shirin fafatawar da suke yi a zabuka dake shirin gudana.

kasuwar saida kayayyakin gwanjo a birnin Bagadaza, bayan harin kunar bakin waken da aka kai a ranar 21 ga watan janairun 2021.
kasuwar saida kayayyakin gwanjo a birnin Bagadaza, bayan harin kunar bakin waken da aka kai a ranar 21 ga watan janairun 2021. AP - Hadi Mizban

Har yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai farmakin, wanda shi ne na biyu mafi muni da aka kai a birnin Bagadaza a cikin wannan shekara, bayan wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da ya halaka akalla mutane 32 a wata Kasuwa cikin watan Janairu, da kungiyar IS ta dauki alhakinsa.

Harin na watan Janairu dai shi ne mafi muni da aka gani a babban birnin kasar ta Iraqi cikin shekaru 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.