Isa ga babban shafi
Iraqi

Fira Ministan Iraqi ya tsallake rijiya da baya a yunkurin yi masa kisan gilla

Fira Mnistan Iraqi Mustafa al-Kadhemi ya tsallake rijiya da baya bayan yunkurin da aka yi na yi masa kisan gilla, inda aka yi amfani da wani jirgin sama mara matuki dauke da bama-bamai, wajen afkawa gidansa dake birnin Bagadaza da sanyin safiyar Lahadin nan.

Firaministan Iraqi Mustafa al-Kadhemi
Firaministan Iraqi Mustafa al-Kadhemi Eliot BLONDET POOL/AFP/File
Talla

Ana dai kyautata zaton harin da aka kaiwa Al-Kadhemi ba zai rasa nasaba da rikicin siyasa kan zaben ‘yan majalisun baya bayan nan a kasar ta Iraqi ba.

Tuni dai Amurka ta yi A-wadai da harin da ta bayyana a amtsayin ta'addanci, yayin da shugaban Iraqi Barham Saleh ya kira harin da yunkurin juyin mulkin da ya sabawa tsarin mulkin kasar.

Tun watan Mayun da ya gabata Kadhemi, mai shekaru 54, ke rike da mukamin na Fira Ministan Iraqi, wanda kuma a ‘yan kwanakin nan ya roki a kwantar da hankula a kasar kafin ya jagoranci wani taro a ofishinsa da ke yankin Bagadaza mai tsananin tsaro, inda aka kai wa farmaki cikin dare.

Bincike dai ya nuna an harba jirage marasa matuka guda uku ne daga kusa da gadar kogin Tigris, amma aka kama biyu daga cikinsu, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.

Cikin wani gajeren bidiyo da ya fitar, Fira Minista Kadhemi ya ce “matsorata sun kaiwa gidana hari, to amma godiya ga A domin babu abinda ya same ni”

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.