Isa ga babban shafi
Iraqi

Iraki ta kakkabo wasu kuraman jiragen saman biyu

Rundunar sojin Iraki ta ce ta kakkabo wasu kuramun jirage biyu dake shawagi a kan sansanin sojin Amurka dake kasar, wata guda bayan an yi yunkurin kai hari sansanin da wani jirgin soja mara matuki.

Jirgin sama mara mutuki na Amurka, 7 ga watan Nuwamba 2020
Jirgin sama mara mutuki na Amurka, 7 ga watan Nuwamba 2020 AFP - WILLIAM ROSADO
Talla

Wannan wani sabon dabarun kai farmaki da mayaka dake samun goyon bayan Iran ke amfani da shi, na dada tada hankalin hukumomin Amurka da Iraki.

Lamarin da yasa Amurka ta sanya wata na'ura domin kakkabo jirage marasa matuki a saman sansaninta na Ain al-Asad, da yake yammacin saharar Iraki, wanda ya yi nasarar dakile wannan hari, kamar yadda rundunar sojin ta bayyana.

Babu dai wata kungiya da ta dauki nauyin wannan hari na ranar Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.