Isa ga babban shafi

FIFA ta ware dala miliyan 150 don ragewa manbobinta radadin corona

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, ta bayyana ware tallafin dala miliyan 150, domin baiwa hukumomin kasashe da yankuna 211 da suke manbobinta, da zummar rage radadin durkushewar tattalin arzikin da annobar coronavirus ta janyo musu.

Tambarin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.
Tambarin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA. Reuters
Talla

Cikin sanarwar da ta fitar a karshen mako, FIFa ta ce kowace hukumar kwallon kafa a matakin kasa za ta samu kason dala dubu 500, idan suka cika ka’idojin cancantar samun tallafin, dake a matsayin kashin farko.

Shugaban FIFA Gianni Infantino yace tallafin na daga cikin shirin da hukumar ta kaddamar a shekarar 2016, na rabawa hukumomin kasashe manbobinta jimillar dala biliyan 1 da miliyan 746, daga shekarar 2019 zuwa 2022.

Tun bayan bulla a birnin Wuhan na China a watan disambar bara da kuma yaduwa zuwa sassan duniya, annobar coronavirus da kawo yanzu ta halaka kusan mutane dubu 200, ta haddasa karyewar tattalin arzikin duniya, fannin wasanni kuma na daga bangarorin da tasirin annobar ya durkusar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.