Isa ga babban shafi
Wasanni-Spain-Corona

Spain ta yiwa wasanni dakatarwar sai baba ta gani

Gwamnatin Spain ta sanar da dakatar da dukkanin wasannin kwallon kafa ciki har da gasar La liga har zuwa lokacin da za ta kammala yakar annobar cutar corona da ke ci gaba da kisa a kasar.

Matakin dakatar da wasannin na cikin tsare-tsaren gwamnatin Spain na ganin ta yaki annobar cutar corona da ke ci gaba da kisa a kasar.
Matakin dakatar da wasannin na cikin tsare-tsaren gwamnatin Spain na ganin ta yaki annobar cutar corona da ke ci gaba da kisa a kasar. REUTERS/Albert Gea
Talla

Tun farkon watan Maris din nan ne hukumar kwallon kafar kasar ta umarci dakatar da wasannin na makwanni 2 da nufin dakile yaduwar cutar, sai dai a yau Litinin ma’aikatar wasannin kasar ta fitar da sanarwar da ke nuna cewa babu ranar dawowa wasannin har sai anga abin da hali ya yi game da cutar ta Corona.

Karkashin gasar ta Laliga dai, yanzu haka Barcelona ce ke jagorancin teburi da maki 58 bayan doka wasanni 27 tazarar maki biyu tsakaninta da babbar abokiyar dabinta Real Madrid da ke matsayin ta biyu.

Matakin na Spain na zuwa bayan gwajin da aka yiwa Dan wasan kwando na Real Madrid da ya tabbatar da yana dauke da cutar ta Corona kwanaki kalilan bayan mutuwar tsohon shugaban kungiyar Lorenzo Sanz.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.