Isa ga babban shafi
Wasanni

Annobar Coronavirus ta halaka tsohon shugaban Real Madrid

Tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Lorenzo Sanz ya mutu a ranar asabar, yana da shekaru 76 bayan gajeruwar jinyar da yayi a asibiti sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus.

Tsohon shugaban Real Madrid Lorenzo Sanz.
Tsohon shugaban Real Madrid Lorenzo Sanz. Reuters
Talla

Sanz ya shugabancin kungiyar ta Real Madrid daga shekarar 1995 zuwa 2000, wanda a karkashinsa kungiyar ta lashe kofin gasar zakarun Turai sau biyu.

A wani labarin kuma har yanzu mafi akasarin ‘yan wasan Real Madrid ciki har da kaftin sinsu Sergio Ramos na a killace, domin tabbatar da lafiyar cewa basa dauke da kwayar cutar murar ta Coronavirus ko Covid-19.

A halin da ake ciki baki dayan wasannin kwallon kafa da na sauran fannoni na hutun dole a fadin duniya saboda yaduwar annobar Coronavirus da kawo aynzu ta kashe sama da mutane dubu 14 da kuma kama wasu sama da dubu 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.