Isa ga babban shafi
Wasanni-Coronavirus

Kungiyoyin Brazil sun mayarda filayensu asibitoci don yakar Coronavirus

Manyan kungiyoyin kwallon kafa dake Brazil sun soma mika filayensu ga hukumomin lafiyar kasar domin mayar da su asibitocin wucin gadi, a matsayin tasu gudunmawar wajen yakar annobar Coronavirus da ta addabi duniya.

Daya daga cikin filayen kwallon kafa a Brazil da aka mikawa hukumomin lafiya don samar da asibitocin wucin gadi.
Daya daga cikin filayen kwallon kafa a Brazil da aka mikawa hukumomin lafiya don samar da asibitocin wucin gadi. AFP
Talla

Rahotanni sun ce daga lokacin da aka dakatar da gasar kwallon kafar Brazil saboda annobar zuwa yanzu, sama da rabin kungiyoyin kwallon kafar kasar sun mikawa hukumomin lafiya filayensu, a dai dai lokacin da hukumomin ke fafutukar fadada wuraren kula da lafiyar jama’a a biranen Sao Paulo da kuma Rio de Janeiro masu yawan al’umma.

A baya bayan nan ne kuma kungiya mai rike da kofin gasar kwallon kafar ta Brazil Falmengo ta sanar da mika katafaren filinta na Maracana ga ma’aikatar lafiyar kasar.

Yayinda hukumomin lafiyar Sao Paulo, birni mafi girma a Brazil suka bayyana shirin samar da gadajen kwantar da marasa lafiya akalla 200, a filin wasa na Pacaembu, domin sassauta nauyin dake kan asibitocin birnin.

Yanzu haka dai mutane dubu 1 da 128 suka kamu da cutar murar Coronavirus a Brazil, wasu 18 kuma suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.