Isa ga babban shafi
Coronavirus

Ibrahimovic ya kafa gidauniyar Coronavirus

Tauraron kwallon kafar Sweden kuma dan wasan kungiyar AC Milan Zlatan Ibrahimovic ya kaddamar da gidauniyar Dala miliyan guda domin taimaka wa gwamnatin Italiya shawo kan matsalar cutar coronavirus.

Zlatan Ibrahimovic
Zlatan Ibrahimovic AC Milan REUTERS/Daniele Mascolo
Talla

A sakon da ya aike ta instagram, Ibrahimovic ya ce, Italiya ta ba shi duk abin da yake bukata a rayuwa, saboda haka lokaci ya yi da shi ma zai taimaka mata wajen nuna mata so da kauna a wannan yanayi da ta samu kanta a ciki.

Ibrahimovic ya bukaci abokansa da kwararrun ‘yan wasa daga kowanne bangare da kuma jama’ar da ke da niyyar bada gudumawa da su taimaka wajen bada gudumawar da za a mika wa hukumomin lafiyar Italiya.

Dan wasan ya ce, yanzu haka likitoci da masu taimaka musu na sadaukar da rayukansu domin ceto rayukan jama’a, saboda haka ya zama wajibi sauran jama’a suma su bada tasu gudumawar.

A karshe ya ce, abin tunawa shi ne, idan cutar ba ta kai ga Zlatan ba, Zlatan zai kai gare ta wajen taimaka wa a murkushe ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.