Jam’iyyar Laurent Gbagbo ta ayyana shi a matsayin dan takara a saben 2025
Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire kuma jigo a bangaren adawa ga ShugabanAlassane Ouattara wanda a hukumance bai cancanta ya tsaya takara a kasar ba, ya amsa goron gayata na zama dan takara a zaben shugaban kasa na shekara ta 2025, a karkashin jam'iyyarsa ta PPA-CI .
Wallafawa ranar:
Tsohon Shugaban kasar Laurent Gbagbo "ya amince da zama dan takarar jam'iyyar PPA-CI a zaben shugaban kasa na 2025", sanarwa da suka fitar yan lokuta vayan kamala taron shugabanci a karkashin inuwar wannan jam’iyya.
Laurent Gbagbo ya shugabanci kasar ta Cote D’Ivoire kama daga shekara ta 2000 zuwa 2011,rikicin zabe na lokaci ya sa aka kama shi da kuma tisa keyar sa zuwa kotun hukunta manyan laifuka ,wacce ta kuma wanke shi daga duk wasu tuhume-tuhume da ake yi masa.
Bayan dawowarsa kasar Shugaba Ouattara ya yi masa afuwa duk da cewa kotun ta zartas da hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari a kasarsa a shekara ta 2010, ba tareda soke ko shafe laifukan da ake tuhumar sa ba musaman hari tare da kwashe kudi a babban bankin yammacin Africa da aka sani da BCEAO a wancan lokaci.
A nata bangaren, jam'iyyar Democrat ta Cote d'Ivoire (PDCI), babbar jam'iyyar adawa, ta zabi dan takara, Tidjane Thiam, a watan Disamba watan da ya gabata.
Shi ko Alassane Ouattara bai ce uffan ba game da yiwuwar tsayawa takarar shugabancin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu