Isa ga babban shafi

Ouattara ya gana da Gbagbo da Bédié don warware rikicin siyasar Cote d'Ivoire

Shugaban Kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya karbi bakuncin tsoffin shugabannin kasar biyu da suka gabace shi, Laurent Gbagbo da Henri Konan Bédié ranar Alhamis, ganawa irinsa ta farko cikin shekaru goma sha biyu, a wani mataki na warware rikicin siyasar kasar.

Shugaban Kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya karbi bakuncin tsoffin shugabannin kasar biyu da suka gabace shi, Laurent Gbagbo da Henri Konan Bédié jiya Alhamis, ganawa irinsa ta farko cikin shekaru goma sha biyu, a wani mataki na warware rikicin siyasar kasar.
Shugaban Kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya karbi bakuncin tsoffin shugabannin kasar biyu da suka gabace shi, Laurent Gbagbo da Henri Konan Bédié jiya Alhamis, ganawa irinsa ta farko cikin shekaru goma sha biyu, a wani mataki na warware rikicin siyasar kasar. © Issouf SANOGO / AFP - Montage RFI
Talla

Shugaban na Code d’Ivoire Alasane Ouattara yayin ganawar kusan sa’a daya da rabi da magabatan nasa biyu wato Laurent Gbagbo da Henri Konan Bédié da basa ga maciji da juna.

A karshen taron na su ne jiga-jigan ‘yan siyasar Ivory Coast suka fitar da wata sanarwar hadin guiwa, wanda tsohon shugaban kasar Laurent Bagbo karamin cikinsu ya karanta, inda aka ciki suka sanar da kawo karshen rikicin siyasar da ke tsakaninsu domin ciyar da kasar gaba.

Shugaba Alassane Ouattara ya bukaci magabatan nasa suyi amfani da kwarewarsu wajen bashi shawara na gari domin ciyarar da kasarsu gaba, inda yayi alkawarin tuntubarsu akai-akai.

Yace ganawar batu ne dake kunshe cikin kudirin da aka gabatar lokacin taron sulhunta ‘yan kasar, kuma shekara guda tun bayan komawar Laurent Gbagbo gida bayan samun ‘yanci daga kotun hukunta manyan laifuka ICC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.