Laurent Gbagbo ya kaddamar a sabuwar jam'iyya a Cote d'Ivoire
Tsohon Shugaban kasar Cote D’Ivoire Laurent Gbabgbo da ya dawo kasar a watan yunin shekarar bana bayan share kusan shekaru 10 a tsare,a yau asabar ya kudiri aniyar kafa sabuwar jam’iyya mai suna PPA-CI wato jam’iyyar al’umar Afrika ta Cote D’ivoire.
Wallafawa ranar:
Shirin na tsohon Shugaban kasar na zuwa a dai dai lokacin da magoya bayan sa ke shirya taron szamar da wannan jam’iya a birnin Abidjan ,inda kusan magoya baya da wakilai 1.600 za su rattaba hannu tareda yin na’am wajen samar da wannan jam’iyya da za agoga da ita a zaben kasar na shekara ta 2025.
A wannan taro da za rufe gobe lahadi ,maid akin tsohon Shugaban kasar Simone Gbagbo wacce ta taka muhimiyar rawa wajen samar da jam’iyyar farko ta Shugaba Gbagbo wato FPI a shekara 1982 ,ba ta halaraci zaman ba bisa dalilai, inda wasu rahotanni ke dada nuni cewa ta na ziyara Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo yanzu haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu