Isa ga babban shafi

Gwamnatin Cote d'Ivoire ta yi wa tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo afuwa

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya yi afuwa ga tsohon shugaban kasar, Laurent Gbagbo, wanda har yanzu yake fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari, sakamakon samunsa da laifin tada tarzoma a shekara ta 2018.

A shekarar 2021 kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta wanke tsohon shugaba Lauren Gbagbo daga zargin tayar da rikicin soyasar a Cote d'Ivoire.
A shekarar 2021 kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta wanke tsohon shugaba Lauren Gbagbo daga zargin tayar da rikicin soyasar a Cote d'Ivoire. AFP - ISSOUF SANOGO,SIA KAMBOU
Talla

"Domin karfafa hadin kan al'umma, na rattaba hannu kan wata doka ta yin afuwa ga tsohon shugaban kasa," in ji Ouattara a wani jawabi da ya yi na bikin cika shekaru 62 da samun 'yancin kan kasar.

Ya kuma bukaci a bude asusun ajiyar Gbagbo da aka rufe tun farko, da kuma biyansa dukkanin hakkokin sa da ke hannun gwamnati.

Shugaban ya kuma rattaba hannu kan wata doka ta sakin wasu makusantan Gbagbo biyu, wato tsohon hafsan sojin ruwa Vagba Faussignaux da tsohon kwamandan wata babbar runduna ta Jandarma, Jean-Noel Abehi, wadanda  aka same su da hannu a rikicin bayan zaben da ya gudana a kasar.

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta wanke Gbagbo daga zargin aikata laifukan yaki a lokacin yakin basasar shekara ta 2011 da ya barke bayan ya ki amincewa da nasarar Ouattara a zaben shugaban kasa.

Sai dai a shekara ta 2018, wata kotu a Ivory Coast ta yanke wa Gbagbo daurin shekaru 20, lokacin da baya kasar, kan wawure dukiyar da aka yi wa babban bankin kasar a lokacin rikicin siyasa da aka yi a kasar.

Bayan kotun ta ICC ta wanke Gbagbo, inda ya koma kasar daga gudun hijira a shekara ta 2021, tsohon sojan mai shekaru 77 ya danyi sanyi a lamuran siyasar Cote d'Ivoire.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.