Isa ga babban shafi
Afrika

Shugaba Macron zai gana da Alassane Dramane Ouattara a Paris

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai gana da takwaransa na Ivory Coast Alassane Ouattara yau juma’a a fadar Elysee da ke birnin Paris a wani lokaci da ake fuskantar rarrabuwar kawuna a kasar biyo bayan tsayawa takara da shugaba Outtara ya yi a baya.

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara.
Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Babu dai cikakken bayani kan batun da shugabannin biyu za su tattauna yayin ganawar ta yau, sai dai akwai yiyuwar ganawar ta tabo batun tazarce ko neman karin wa’adin mulki zagaye na 3 da Alassane Ouattara ke yi yayin zaben kasar na watan Oktoba mai zuwa. Ranar biyar ga watan Maris da ta gabata, shugaban Faransa Emmanuel Macron a hukumance ya bayyana farin cikin sa da kuma yabawa shugaba Ouattara da ya sanar da cewa ba zai sake shigar da takarar sa a zaben kasar ba, kafin daga bisali ya yi amey ya lashe musaman ranar 6 ga watan da ya shude, gum daga bangaren hukumomin Faransa na dada tayar da hankulan yan adawa a kasar ta Cote D’ivoire.

A budadiyar wasika daga yan adawa na kasar ta Cote D’ivoire, wasikar da Pascal Affi N’guessan ya rubuta, gungun yan adawar sun bukaci Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana matsayin sa da na kasar sa Faransa dangane da wannan tsari daga Shugaba Ouattara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.