Na hannun daman Laurent Gbagbo, Charles Ble Goude ya samu izinin komawa gida
Tsohon na hannun daman shugaban kasa a lokacin mulkin Laurent Gbagbo na Ivory Coast wato Charles Ble Goude ya shaidawa kamfanin dilancin labaran Faransa na AFP cewa zai koma gida a wata mai zuwa domin shiga cikin shirin sulhun kasar, bayan da aka wanke su daga laifukan cin zarafin bil adama.
Wallafawa ranar:
Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ne ya amince da ranar ta 26 ga watan Nuwamba, a matsayin ranar da Ble Goude zai koma gida.
Tsohon shugaba Gbagbo kuwa ya koma gida Abidjan ne a watan Yunin shekarar 2021 amma Ble Goude ya jira har sai da fadar shugaban kasa ta bashi dama.
A watan Maris na shekarar 2021, kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta wanke Ble Goude da Gbagbo daga laifukan cin zarafin bil adama yayin rikicin siyasar da ya barke a Ivory Coast a shekarar 2010-2011, bayan da Laurent Gbagbo ya ki amincewa da shan kaye a zaben da Ouattara yayi nasara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu