Isa ga babban shafi

Kotun ICC ta bayar da umarnin a biya mutum 50,000 diyya a Uganda

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta bayar da umarnin a biya kusan mutane 50,000 da kisan kiyashin Dominic Ongwen ya shafa a Uganda diyyar sama da Yuro miliyan 52.

Dominic Ongwen, lokacin da ya bayyana gaban kotun ICC.
Dominic Ongwen, lokacin da ya bayyana gaban kotun ICC. © ICC-CPI
Talla

Alkalan kotun sun ce Ongwen wanda ya shiga aikin soji tun yana yaro, har ya samu shiga matakin manyan kwamandojin yaki na Lord’s Resistance Army, ba shi da abin da zai iya biyan diyyar, maimakon hakan sai kotun ta nemi asusun tallawa wadanda abin ya rutsa da su da ya biya wadannan kudade.

Kotun ta ce za a bayar da diyyar Yuro 750 ga duk wanda aka azabtar a wancan lokaci da kuma gyara wuraren da aka binne wadanda kisan ya rutsa da su.

An yanke wa Ongwen hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari a shekarar 2021 bayan samunsa da aikata laifukan yaki 60 da suka kunshi cin zarafin bil adama ta hanyar aikata fyade, kisa da kuma sace yara, inda a halin yanzu yake ci gaba da zaman gidan yari a kasar Norway.

A karkashin jagorancin Joseph Kony, kungiyar ta LRA ta yi wa 'yan kasar ta Uganda ta'addanci kusan shekaru 20 a lokacin da take yakar gwamnatin shugaba Yoweri Museveni.

An dai kawar da mayakan, amma Kony ya kasance daya daga cikin wadanda kotun ICC ke nema ruwa a jallo.

Asusun da aka ware domin tallafawa mutanen da cin zarafin Ongwen ya shafa, ya dogara ne kan gudun mowar da za a mika masa a shekarar bara, kuma ya zuwa yanzu an tara kasa da Yuro miliyan 20 a cikinsa, don haka ne ma kotun ta ce sai an kara azamar tallafawa asusun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.