Isa ga babban shafi

Harin ta'addanci ya hallaka mutane kusan 30 a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

Wasu da ake zargin mayaka masu ikirarin jihadi ne sun halaka mutane 26 a wani harin da suka kai cikin dare a garin Oicha na gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, kamar yadda magajin garin birnin ya bayyana a jiya Talata. 

Guda daga cikin sojojin da ke aiki a yankin Oicha na jamhuriyar dimokradiyyar Congo
Guda daga cikin sojojin da ke aiki a yankin Oicha na jamhuriyar dimokradiyyar Congo © JOHN WESSELS / AFP
Talla

Mahukuntan yankin sun danganta kisan mayakan kungiyar Allied Democratic Forces (ADF), kungiyar da ta samo asali daga Uganda, kuma ta yi mubayi’a  ga kungiyar IS. 

Maharan sun aiwatar da aika-aikar tasu ne da takkuba a maimakon bindigogi saboda su  kaucewa sojojin da ke yankin, wadanda ka iya jin karar bindiga, a cewar kakakin sojin yankin, Anton Mwalushayi, wanda ya ce harin ramuwa gayya ne ga luguden wutar da sojojin kasar suka yi wa mayakan ADF  kwanakin baya. 

Da ya ke jawabi magajin garin Oicha dake arewacin Kivu Nicholas Kikuku yace maharan sun fara kai harin ne tun karfe 11 na cikin daren jiya, inda suka kashe mutanen tare da jikkata wasu guda 4 da yanzu haka suke asibiti.

Mazauna yankin sun nuna fargaba game da wannan sabon salon harin da ‘yan ta’addar suka bullo da shi, a cewar su zai hana jami’an tsaro jin karar bindiga don kai musu dauki.

Wannan sabon hari na zuwa ne bayan da kasashen Jamhuriyar dimokradiyyar Congo da Uganda suka sake karfafa alakar sojin su da ke yaki da ADF.

Ko a watan da ya gabata rundunar sojin Uganda ta sanar da cewa ta kashe ‘yan ta’adda kimanin 560 tare da lalata sansanin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.