Isa ga babban shafi

Akwai yiwuwar Rasha ta kulla alaka da Chadi bayan ziyarar Deby a Moscow

Shugaban Chadi Mahamat Idris Deby ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a ziyarar da ya kai Moscow jiya Laraba, ziyarar da ke bayyana yiwuwar kulluwar alaka tsakanin kasar ta gabashin Turai ta takwararta ta tsakiyar Afrika.

Ganawar Mahamat Idris Deby na Chadi da shugaba Vladimir Putin na Rasha a birnin Moscow.
Ganawar Mahamat Idris Deby na Chadi da shugaba Vladimir Putin na Rasha a birnin Moscow. © Mikhail Metzel / AP
Talla

Ziyarar ta Deby da ke zuwa mako guda bayan makamanciyarta da Firaministan Nijar ya kai Moscow, har zuwa yanzu babu cikakken bayani kan manufar ziyarar ko kuma yiwuwar kulla yarjejeniya ko kawance tsakanin Rashan da Chadin wadda ke matsayin kawa ga Faransa.

Yayin ganawar shugabannin biyu Putin ya yabawa Deby game da namijin kokarinsa wajen tabbatar da zaman lafiya a Chadi, yana mai cewa Rasha na sanya idanu sosai game da yanayin tsaron Chadi da ma halin da kasar ke ciki.

A cewar Putin akwai yiwuwar iya gudanar da zaben raba gardama kan kundin tsarin mulkin na Chadi amma Rasha na da kwarin gwiwar cewa zabe zai gudana yadda ya kamata lura da yadda al’amura suka daidaita a kasar.

Yayin zantawar tasu wadda aka haska kai tsaye ta gidan talabijin, Deby ya jajantawa Putin game da kakkabo jirgin Sojin kasar da Ukraine ta yi a yankin Belgorod da ya kasha mutane 74 a jiyan.

Deby wanda ya fara jagorancin Chadi a shekarar 2021 bayan mutuwar mahaifinsa a fagen daga, ya sauya fasalin siyasar kasar musamman wajen sasantawa da ‘yan tawaye da kuma bangarorin adawa da aka jima ana takun saka tsakaninsu da mahaifinshi.

Chadi na matsayin kasa ta karshe da Faransa ke da kyakkyawar alaka da ita a yankin Sahel bayan da Rasha ke ci gaba da fadada ikonta a yankin musamman bayan juyin mulkin da kasashe 3 na Mali Burkina Faso da kuma Nijar suka gani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.