Isa ga babban shafi

'Yan majalisar dokokin Chadi sun amince da jagoran adawa a matsayin fira minista

‘Yan majalisar dokokin Chadi da gwamnatin sojin kasar ta nada sun amince da tsohon madugun ‘ya adawa, Succes a matsayin Fira minista da gagarumin rinjaye a wata kuri’ar da suka kada.

Tsohon madugun 'yaan adawan Chadi, Succès Masra.
Tsohon madugun 'yaan adawan Chadi, Succès Masra. © Les Transformateurs
Talla

Masanin tattalin arzikin mai shekaru 40, ya dawo daga gudun hijira a watan Nuwamba bayan cimma yarjejeniya da gwamnatin sojin kasar, wadda ta ba shi tabbacin zai ci gaba da shiga harkokin siyasar. 

Jagoran jam’iyyar Transformer ya kasance mai matukar caccakar iyalan Deby, wadanda suka shafe shekaru sama d 30 a kan karagar mulkin kasar. 

Masra ya lashe kashi 95 na kuri’ar da ‘yan majalisar dokokin 173 suka kada a ranar Juma’a, kamar yadda tashar talabijin na gwamnatin kasar ta ruwaito. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.