Isa ga babban shafi

Janar-janar din Sudan biyu sun sake tsagaida wuta bayan kazancewar rikici

Manyan hafsoshin sojin Sudan biyu da ke fada da juna sun sake amince wa da sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta na sa'o'i 72 daga wannan Lahadi, kamar yadda masu shiga tsakani na Amurka da Saudiyya suka sanar.

Janar -janar din Sudan biyu Abdel Fatah Alburhan da mataimakinsa Hamdan Daglo.
Janar -janar din Sudan biyu Abdel Fatah Alburhan da mataimakinsa Hamdan Daglo. AFP - ASHRAF SHAZLY
Talla

Sanarwar na zuwa ne bayan kazamin fada da aka gwabza da kuma munanan hare-hare ta sama da aka kaddamar a birnin Khartoum da kuma rahotannin kwararrar ‘yan  gudun hijirar da suka samu raunuka daga Darfur zuwa kasar Chadi.

Hare-haren jiragen sama sun kashe fararen hula 17, ciki har da yara biyar, a babban birnin kasar jiya Asabar, yayin da ma'aikatan lafiyar kasar Chadi suka bayar da rahoton daruruwan wadanda suka jikkata daga Darfur na neman magani a kasar.

Wannan dai ba shi ne karon farko da bangarorin biyu ke amince da tsagaita wuta ba, a yakin da aka kwashe watanni biyu ana gwabzawa, amma kuma sai ta wargaje, ciki harda wanda Amurka ta kakabawa janar-janar din biyu takunkumi, duk da haka yunkurin da aka yi na baya-bayan nan ya ruguje a karshen watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.