Isa ga babban shafi

Shugaban Chadi ya nada jagoran 'yan adawa a matsayin firaminista

Shugaban Rikon Kwaryar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby Itno ya nada tsohon jagoran 'yan adawa wanda ya koma kasar daga gudun-hijira a baya-bayan nan a matsayin firaministansa.

Jagoran 'yan adawar Chadi, Succès Masra.
Jagoran 'yan adawar Chadi, Succès Masra. AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Succes Masra, shugaban jam'iyyar Transformers, ya jima yana nuna adawarsa ga mulkin iyalan gidan Deby, amma ya koma Chadi a cikin watan Nuwamban da ya gabata bayan ya cimma wata yarjejeniya da jagororin sojin kasar.

Gabanin gudanar da zaben raba gardama kan sauya kundin tsarin mulkin kasar a watan jiya wanda ya samu goyon bayan kashi 86 na masu kada kuri'a, Masra ya fito bainar jama'a yana rokon magoya bayansa da su goyi bayan samar da sabon kundin tsarin mulki, yayin da ake sa ran sakamakon zaben zai bude hanyar gudanar da zabe a kasar.

Sakatare Janar na fadar shugaban kasa, Ahmat Alabo, shi ne ya sanar da nadin Succes Masra a matsayin firaminista ta kafar talabijin mallakin gwamnatin kasar a yau Litinin.

Ya yi gudun hijira ne jim kadan da zanga-zangar ranar 20 ga watan Oktoban 2022 wadda aka gudanar da ita don nuna adawa ga gwamnatin mulkin soji da ta tsawaita wa'adin mika mulki ga farar hula da shekaru biyu.

Hukumomin kasar sun ce, kimanin mutane 50 sun rasa rayukansu a wannan rana ta zanga-zanga, yayin da 'yan adawa da kuma kungiyoyin kasa da kasa masu zaman kansu suka ce, mutanen da aka kashe sun kai daga 100 zuwa 300.

Harbin bindigar sojoji da 'yan sanda ne dai, ya yi sanadiyar mutuwar akasarin masu zanga-zangar a wancan lokacin a birnin N'Djamena

A ranar 3 ga watan Nuwamba ne, Masra ya dawo daga gudun hijira sakamakon yarjejeniyar da aka cimma a birnin Kinshasa a ranar 31 ga watan Oktoba wadda ta ba shi tabbacin 'yancin gudanar da harkokinsa na siyasa a Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.