Isa ga babban shafi

Masar ta sha alwashin baiwa Somalia kariya daga barazanar Habasha

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na Masar ya yi alkawarin cewa kasar shi za ta yi iyakar kokarinta wajen baiwa Somalia cikakkiyar kariya daga dukkanin barazanar da ta ke fuskanta daga makwabta, kalaman da kai tsaye ke nufin yarjejeniyar yankin Somaliland da Habasha.

Shugaba Abdel Fattah al-Sissi na Masar.
Shugaba Abdel Fattah al-Sissi na Masar. © AP/Christophe Ena
Talla

Sisi yayin zantawarsa da shugaba Hassan Sheikh Mohamud a birnin Alqahira, ya ce Masar ba za ta goyi bayan duk wani yunkuri da zai kalubalanci matsayin Somalia a matsayin kasa mai cikakken iko da yankin Somaliland mai kwarya-kwaryar ‘yanci ba.

Al Sisi ya yi watsi da ingancin yarjejeniyar da yankin Somaliland ya kulla da Habasha wanda zai baiwa Addis Ababa damar amfani da gabar ruwan yankin baya ga kwancen tsaro tsakanin bangarorin biyu a baya-bayan nan.

A cewar shugaban na Masar, ko shakka babu za su taimakawa Somalia wajen samun cikakken iko da dukkanin yankunan da ke karkashinta.

Kafofin yada labarai sun ruwaito al-Sisi na shelar cewa Masar ba za ta lamunci ganin ana yiwa Somalia duk wata barazana ba, musamman ma a irin wannan lokaci da Somaliyan ta nemi taimakonta.

Yankin Somaliland mai kwarya-kwaryar ‘yanci da ke gab da Gulf of Aden a shekarar 1991 ne ya sanar da ballewa daga Somalia tare da ayyana ‘yancin kai wanda ya kai ga gagarumin rikici tsakanin bangarorin biyu.

Yankin na ci gaba da tafiyar da harkokinsa ba tare da samun goyon bayan kasashen duniya ba, kuma a farkon shekarar nan gwamnatin yankin ta yi nasarar kulla yarjeniyoyi da Habasha lamarin da ya haddasa tarnaki tsakanin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.