Isa ga babban shafi

Somalia ta gargadi Habasha kan kulla yarjejeniya da Somaliland

Somalia ta gargadi makwabciyarta Habasha game da yarjejeniyar da ta kulla da mahukuntan yankin Somaliland mai kwarya-kwaryan ‘yanci wanda zai baiwa Addis Ababa damar ratsa tekun Maliya ta hanyar amfani da gabar ruwan yankin.

Shugaban yankin Somaliland, Muse Bihi Abdi tare da Firaminista Abiy Ahmed na Habasha yayin kulla yarjejeniyar hada-hadar ruwa ranar Litinin 1 ga watan Janairu.
Shugaban yankin Somaliland, Muse Bihi Abdi tare da Firaminista Abiy Ahmed na Habasha yayin kulla yarjejeniyar hada-hadar ruwa ranar Litinin 1 ga watan Janairu. REUTERS - TIKSA NEGERI
Talla

Firaministan Somalia Hamza Abdi Barre ya yi gargadin cewa ko shakka babu kasar ba za ta zuba ido haramtacciyar yarjejeniyar ta yi tasiri ba, wadda tuni bangarorin biyu suka sanya hannu tsakanin Firaminista Abiya Ahmed da Muse Bihi Abdi tun a Litinin din da ta gabata.

Yarjejeniyar ta ranar Litinin na nuna cewa kai tsaye Habasha za ta rika amfani da tashar jiragen ruwan yankin mai kwarkwarya ‘yancin cin gashin kai, ta yadda Addis Abba za ta karkata hada-hadarta daga tashar jiragen ruwan Djbouti zuwa yankin, batun da bai yi wa Somalia dadi ba.

Zuwa yanzu dai Somalia ta sanar da janye jakadanta daga Habasha bayan kiran yarjejeniyar da cin fuska daga makwabciyarta inda Firaminista Hamza Abdi Barre, ke cewa kasar za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen bayar da kariya ga ilahirin iyakokinta ta ruwa tare da kange duk wata haramtacciyar hada-hada tsakanin Somaliland da Habasha.

Kai tsaye Habasha za ta rika samun damar isa ga tekun Maliya ta hanyar amfani da gabar ruwan na Somaliland wanda zai kawo mata sauki fiye da yadda ta ke amfani da tashar jiragen ruwan Barbera a baya.

Sai dai a jawabin na Firaminista Abdi Berre ya nanatawa Habasha cewa har yanzu yankin na Somaliland na karkashin ikon Somalia ne wanda ke nuna babu kasar da ke da zarafin iya kulla yarjejeniya ta kai tsaye da mahukuntan yankin kuma yin hakan kai tsaye kalubalantar ikon Mogadishu ne.

A cewar Somalia ta mika koke gaban Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afrika da kuma kungiyar kasashen Larabawa dama kungiyar kasashen gabashin Afrika don samun goyon baya wajen baiwa kasar kariya daga haramtacciyar yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.